• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA SAI MUTUM YA MALLAKI KATIN DAN KASA BA NE ZA A MA SA REJISTAR ZABE-INEC

ByYusuf Yau

Apr 5, 2021

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce ba lalle ne sai dan kasa na da katin dan kasa ne zai samu rejistar katin zabe ba.

Shugaban humumar Mahmud Yakubu ya baiyana haka don faiyace ka’idar rejistar zaben.

Mahmud Yakubu ya ce ba lalle sai mutum ya kawo rejistar dan kasa ba, don ita ma ta na cikin jerin shaidu ne da dama da mutum zai iya kawowa don a gane shi da tabbacin shekarun sa sun kai 18 don samun rejistar.

Sauran shaidun sun hada da fasfo, lasisin tuka mota da sauran su. Ya nuna duk shaidar da mutum ya nuna a cikin wadannan za a amince a yi ma sa rejista da ita.

Za a bude cigaba da rejistar a watan yuni.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *