• Fri. Jan 28th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA SABANI TSAKANIN SHUGABA BUHARI DA TINUBU-FADAR ASO ROCK

Fadar Aso Rock ta ce ba sabani kamar yanda a ke yayatawa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da uban jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.

A sanarwa daga mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu, ta ce fadar na mutanta jam’iyyar APC kuma batun wai an samu sabani tsakanin ginshikan jam’iyyar biyu ba gaskiya ba ne.

Fadar ta ce wadanda su ka yada wannan labari masharranta ne kawai da ke da mummunar manufa.

Fadar ta ce masu yada jita-jitar na son farraka kan jama’a kan manufofin gwamnatin, amma ba za su samu nasara ba.

Kazalika ba lalle ba ne a rika ganin Tinubu a fadar koyaushe don shi ba dan majalisar zartarwar gwamnati ba ne, don haka ba hujja ba ce rashin ganin sa a fadar a kai a kai ya juya ya zama samun sabani ne tsakanin sa da shugaba Buhari.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *