• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA SA FARA NEMAN RABA NAJERIYA SAI IN DAN AREWA NA MULKI-SHEIKH BALA LAU

Shugaban kumgiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce masu tada kayar baya don kafa kasar Biafra ba sa bude wuta ko matsa lamba sai lokacin da dan arewa ya ke karagar mulki.
Sheikh Bala Lau wanda ke yabawa al’ummar arewa musulmi da wadanda ba musulmi ba don hakuri da kaucewa daukar fansa, ya ce masu kashe-kashe don kafa Biafra ba sa la’akari ko ba su san fitinar da yaki ke jawowa kasa ba ne.
A lokacin da ya ke bukatar kara jurewa da kin biyewa masu neman tunzura ‘yan arewa don kunna wutar da ba a san iyakacin ta ba, malamin ya ce musulunci bai yarda mutum ya dau makami kan wanda bai yi ma sa laifin komai ba, hakanan hakkin kare mutane ko bin kadun zalunci da a ka yi mu su na wuyan gwamnati ne.

Imam Bala Lau ya ce yankin arewa ba ya shakkar zama shi kadai a matsayin Najeriya don arzikin da Allah ya yi ma sa, amma masu son tada fitinar ba sa duba irin dukiyar da ‘yan uwan su, su ka tara a arewa ne da kuma irin huldar zamantakewa da ke tsakanin jama’ar sassan biyu tsawon shekaru aru-aru.
Malamin ya goyi bayan matakin da shugaban kasa ke dauka na kwantar da fitinar masu son raba kasa ta yi mu su magana da harshen da su ke ji.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.