• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA RUDANI KAN NEMAN TURA DCP KYARI AMURKA-MALAMI

Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya ce ba wani rudani kan shirin mika DCP Abba Kyari ga Amurka don fuskantar tuhumar alaka da dan damfara Ramon Abbas Huspuppi.
Malami na magana ne da manema labaru a fadar Aso Rock kan bukatar da ya shigar kotu ta ba da izinin tura Kyari Amurka, alhali ga wata kara da hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi ta shigar ta na bukatar a hukunta Kyari kan zargin alaka da fataucin kwaya.
Shari’a na nuna matukar a na shari’ar mutum kan wani laifi a Najeriya, to bisa doka ba daidai ne a dauko batun mika shi kasar ketare ba.
Duk da haka Malami ya ce ba wani abun boye a lamarin don Amurka ta rubuto bukatar a ba ta Kyari don tuhumar da ta ke yi ma sa kuma wannan shi ya say a mika bukatar hakan gaban kotu.
Sashen masu kare Kyari ne su ka dauko batun rashin hurumin mika Kyari Amurka alhali ga wata shari’a da a ke yi ma sa a gida.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “BA RUDANI KAN NEMAN TURA DCP KYARI AMURKA-MALAMI”
  1. I’m curious to find out what blog system you happen to be utilizing? I’m having some small security issues with my latest site and I’d like to find something more safe. Do you have any recommendations?

  2. Thanks for another wonderful article. Where else could anyone get that type of info in such an ideal way of writing? I have a presentation next week, and I’m on the look for such info.

Leave a Reply

Your email address will not be published.