• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA NA SON A MAIDA LAMURAN ZABEN EDO KO A MUTU KO A YI RAI – SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari  ya ce ba ya son ya ga masu ruwa da tsaki a lamarin zaben jihar Edo sun dau dabi’ar ko-a-mutu-ko-ayi-rai a lamarin zaben gwamnan jihar. Shugaban ya ce ba daidai ba ne ‘yan siyasa su shiga neman mulki ko ta halin kaka. Shugaban ya ce ya dau akidar tabbatar da adalcin zabe, amma matukar sauran ‘yan siyasa ba su dau dabi’ar ba, za a iya samun kalubale.

Ba wannan ne karo na farko da shugaban kan furta irin wannan matsaya ba a lokacin da zabe ya tinkaro. Ko a zaben 2019, shugaban ya bukaci jama’a su kada duk gwamnan da su ka ga bay a aikata abun da ya dace kuma ko jam’iyyar sa ne. Duk da haka lokacin da dan takarar APC a Edo Pastor Ize Iyamu ya kawo ma sa gaisuwa a fadar Aso Rock, shugaban ya yi ma sa fatar lashe zaben.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.