Sanata Abdullahi Adamu ya ce ba ya shakkar a gudanar da zabe a tsakanin sa da sauran ‘yan takarar neman shugabancin APC a karshen makwan nan.
Adamu na amsa tambayaoyin manema labaru ne kan raderadin ya fi son a daidaita a fitar da dantakara maimakon kada kuri’a.
Tun fitowar Adamu neman jagorancin APC da shi ne kusan na karshe a baiyana wannan aniya, a ke cewa shugaba Buhari ne ya mara ma sa baya kasancewar sa mai yawan shekaru da rashin shakkar daukar matakai.
Tsohon gwamnan na Nassarawa bai fito kai tsaye ya ce shugaba Buhari na mara ma sa baya ba, amma ya yi jirwaye mai kamar wanka.
Duk da tura takarar yankin arewa ta tsakiya, akalla Abdullahi Adamu na da abokin takara mai karfi daga jihar sa ta Nassarawa wato tsohon gwamna Tanko Almakura.
Adamu ya ce a rayuwar sa ba ya fargabar fadawa kowa gaskiya sai dai sanin furucin da zai yi amfani da shi bisa darajar wanda ya ke yi wa magana.
Dan majalisar wakilai Abdulrazak Namdas na da kwarin guiwar za a sulhunta wajen fitar da sabon shugaban na APC.
Kimanin wakilai 4000 za su halarci babban taron na APC a asabar din nan a dandalin taro na EAGLE da ke Abuja.
BA NA SHAKKAR A GUDANAR DA ZABE A TARON APC-ABDULLAHI ADAMU

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀