• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA NA MAMAKI IN AN CE WASU SUN YI WA SHUGABA BUHARI SAMMU-ABDULKARIM DAIYABU

Shugaban rundunar adalci Abdulkarim Daiyabu ya ce babu mamaki idan an ce an yi wa shugaba Buhari sammu don yanda ya ke gudanar da lamuran sa a baya ya sha bamban da yanzu.

Daiyabu da ya ke jagorantar kungiyar mai zaman kan ta daga helkwatar sa a Kano, ya ce tsammanin da mutane irin sa su ka yi wa shugaba Buhari na jajircewa wajen gyara kasa bai tabbata ba zuwa yanzu sai ma wasu sabbin matsaloli da a ka kara samu.

Dattijon ya ce yanzu noma, kiso, fatauci duk sun zama ba sa yiwuwa ga jama’a don misali manomi in ya je gonar sa a daji zai yi wuya ya dawo gida ba tare da an sace shi ba.

Don haka Daiyabu ya bukaci masu kishin kasa su hada kai don nazarin wata hanyar ta daban mai bullewa da za ta kai kasar tudun mun tsira.

A cewar Daiyabu, shi dai a yanzu ba ya rawar jikin neman ganawa da shugaba Buhari don ya na ganin ko ya fadi wata abu ko ba da wata shawara, wadanda ya zaiyana da ‘yan kabal za su warware ta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *