• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA MU SAMU HUNKUNCIN KOTU NA BIYAN IGBOHO NAIRA BILIYAN 20 BA-DSS

 

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta ce ba ta samu hukuncin kotu da ta yanke na biyan mai ikirarin kare muradun yarbawa Sunday Igboho ba, bisa samame a gidan sa a Ibadan da hakan ya kai ga musayar wuta da cafke wasu mukarrabai.

Alkali a babbar kotun Oyo a Ibadan Ladiran Akintola ya yanke hukuncin ba da diyya ga Igboho bisa kustawa gidan sa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin rundunar ta DSS Peter Afunanya na cewa ba mamaki kotun ba ta miko hukuncin ga rundunar ba don haka ba zai iya dorar da wani zance a kai ba.

Duk mukarraban Igboho da a ka cafke an sake su, saura biyu da a ke tuhuma da aikata ta’addanci.

Igboho dai na gidan yari a birnin Kotono na Benin don jiran hukunci kan shiga kasar da takardun jabu da zummar arcewa zuwa Jamnus.

 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “BA MU SAMU HUNKUNCIN KOTU NA BIYAN IGBOHO NAIRA BILIYAN 20 BA-DSS”

Leave a Reply

Your email address will not be published.