• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA MU JI DADIN YANDA A KE SAMUN MATSALA TSAKANIN TSOHON GWAMNA MU’AZU BABANGIDA ALIYU DA SASHEN SHUGABANNIN PDP BA – MAGOYA BAYA

ByYusuf Yau

Sep 25, 2020 , ,

Kungiyoyin magoya bayan jam’iyyar PDP sun nuna damuwa ga wani lamari na rashin jituwa tsakanin sashen jam’iyyar PDP da tsohon gwamnan Neja Mu’azu Babangida Aliyu.

A taron da su ka gudanar gidan “LEGACY” da ke Abuja, magoya bayan karkashin Ezejie Chidozie sun ce rasa martaba ginshikan jam’iyyar irin Mu’azu Babangida ka iya kawowa jam’iyyar matsala musamman a jihar Neja.

Sun ce rashin jituwar ta taso ne daga sakataren kudin jam’iyyar Abdullahi Maibasira inda hakan ya sanya rashin gudanar da babbar taron zaben jam’iyyar a jihar Neja.

Abdullahi Maibasira daga Neja wanda a baya tsohon shugaban matasan jam’iyyar PDP ne, yanzu shi ne Ssakataren kudin jam’iyyar.
Magoya bayan sun bukaci shugaban PDP Uche Secondus da sakataren jam’iyyar Sanata Umar Tsauri su binciki lamarin don kawo maslaha.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “BA MU JI DADIN YANDA A KE SAMUN MATSALA TSAKANIN TSOHON GWAMNA MU’AZU BABANGIDA ALIYU DA SASHEN SHUGABANNIN PDP BA – MAGOYA BAYA”
  1. Having read this I thought it was very enlightening. I appreciate you finding
    the time and energy to put this short article together.
    I once again find myself personally spending a lot of time
    both reading and commenting. But so what, it was still worthwhile!

Leave a Reply

Your email address will not be published.