• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA MU FASA KORAR MA’AIKATA A KADUNA BA-GWAMNATIN KADUNA

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce yajin aikin gargadi na kwana 5 da kungiyar kwadago ta shiga a jihar, ba zai firgita gwamnati daga batun korar ma’aikata a jihar ba don rage nauyi kan gwamnati.

Shugabar ma’aikatar ta jihar Bara’atu Muhammad ta baiyanawa manema labaru wannan matsaya yayin da ma’aikatan su ka cika alwashin fara yajin aikin.

Bara’atu ta ce jihar ba za ta firgita a rage yawan ma’aikatan ba.

Shugabar ma’aikatan ta ce ya kamata ma’aikatan su san su na jefa mutane cikin halin damuwa wajen rufe asibitoci da wutar lantarki.

Yayin da ta ke cewa yajin aikin bai shafi lamuran gwamnati ba, Bara’atu ta ce gwamnatin ba za ta yi shayin aiki da dokokin aiki wajen hukunta ma’aikatan ba.

Kwadago ta lashi takobin rashin amincewa da duk wata barazana daga gwamnati kan yajin aikin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.