• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA MAMAKI WASU KASASHE SU BI SAHUN INDUNUSIYA WAJEN DAKATAR ZUWA HAJJIN BANA

Alamu na nuna wasu kasashe za su bi sahun kasar Indunusiya wajen dakatar haramar aikin hajjin bana na hijra 1442.

Indunusiya wacce ta fi kowace kasa yawan tura alhazai kasar Saudiyya, a bana ta sanar da dakatar da niyyar zuwa bisa dalilin kare ‘yan kasar daga korona bairos.

Kasar kan samu kujeru dubu 232 da ya sanya ta ke gaba da kowace kasa yawan alhazai a duniya.

Yanzu haka kasar ta na amfani da allurar rigakafin korona daga kasar Sin.

Hukumomin Indunusiya sun ce sun dau matakin bayan tuntubar duk masu ruwa da tsaki na lamuran aikin hajji.

Wannan ya zama shekara biyu kenan a jere Indunisiya za ta kara jira ba tare da zuwa aikin hajjin ba don wannan annoba.

Ba mamaki wani dalilin shi ne ko am ba da damar tafiya hajjin, to zai zama ‘yan alhazai kalilan ne za su samu dama.

Indunusiya na da tsarin adashen biyan kujerar hajji da sai mutum ya share fiye da shekara 20 ya na jiran damar sa ta tafiya hajji ta iso.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *