• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA KWARIN GUIWA KAN UKRAINE BAYAN ZANTAWAR PUTIN DA BIDEN

Zantawar shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Joe Biden ba ta sanya samun kwarin guiwa kan kaucewa mamaye Ukraine din ba.
Kakakin cibiyar tsaron Amurka PENTAGON Mr.John Kirby na nuna sanyin guiwa kan zantawar sa’a daya ta wayar tarho tsakanin shugaba Biden da shugaba Putin.
Kirby ya shaidawa gidan talabijin na FOX cewa babu alamar shugaba Putin na da aniyar sauya manufa kan shirin mamaye kasar Ukraine.
Mai ba da shawara kan tsaro na Amurka Jake Sullivan ya ce Rasha na gab da kai hari inda za ta fara sauke boma-bomai da makamai masu linzami a kan Ukraine, inda daga nan sojojin kasa za su biyo baya da hakan zai haddasa kashe fararen hula.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.