• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA ARCEWA NA YI NIYYAR YI BA LOKACIN DA NA AJIYE MULKI-OBIANO

Tsohon gwamnan jihar Anambra Willie Obiano ya ce ba niyyar arcewa daga Najeriya ya yi ba lokacin da ya ajiye mulki da mika ragama ga sabon gwamnan Charles Soludo.
In za a tuna jami’an hukumar yaki da cin hanci EFCC sun cafke Obiano a filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed a Lagos.
Da ya ke magana ta hanyar lauyan sa da Jaridar PREMIUM TIMES, Obiano ya ce ya na da ganin likita ne a birnin Houston na Amurka don haka ya ke gaggawar tafiya don a duba shi.
Obiano tun a Yunin bara, ya ce a ka fara duba shi don haka ya ke son ya isa Amurka don fara ganin likita da zai dauke shi mako 8.
Ba a fadi cutar da ke damun Obiano ba, amma an tsegunta cewa cutar daji ce.
Obiano wanda a ke tuhuma da badakalar naira biliyan 42 na jihar Anambra, ya samu beli amma ba shi da damar ficewa waje don an karbe fasfo din sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “BA ARCEWA NA YI NIYYAR YI BA LOKACIN DA NA AJIYE MULKI-OBIANO”
  1. Thank you a lot for sharing this with all people you actually recognize what you are talking approximately! Bookmarked. Please additionally consult with my web site =). We will have a hyperlink change agreement among us!

Leave a Reply

Your email address will not be published.