• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

BA A BANI SHAWARA NA DAU WIKE MATAIMAKI BA – ATIKU

ByNoblen

Jul 24, 2022

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa Atiku Abubakar ya ce kwamitin jam’iyyar bai mika ma sa sunan gwamnan Ribas Nyesom Wike ya dauke shi mataimakin takarar sa ba.
Atiku Abubakar ya na karin haske ne a zantawa da gidan talabijin na Arise kan yanda ya dauki gwamnan Delta Ifeanyi Okowa maimakon Wike.
Atiku ya ce kwamitin mutum 17 da ya yi aikin taya shi zabar mataimakin bai hada da sunan Wike ba.
Shugaban kwamitin gwamnan Binuwai Samuel Otom ya nuna bacin ran rashin daukar Wike har ya ke ganin ya zama wajibi Atiku ya sulhunta da Wike.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.