• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SIYASA: AUREN ‘YAR NUHU RIBADU YA HADA MANYAN MASU ADAWA DA JUNA WAJE DAYA

Manyan ‘yan siyasar Najeriya daga na gwamnatin APC mai mulki zuwa PDP mai adawa sun taru cunkus a anguwar Aso Drive Abuja don shaida daura auren ‘yar tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci Nuhu Ribadu ga dan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar.

Duk da sabani tsakanin Nuhu Ribadu da Atiku Abubakar kan zargin almundahana, hakan bai hana ‘ya’yan su sun kulla soyaiya mai zafi su ka gamsar da iyayen su a ka daura mu su aure ba.


Atiku wanda shi ya yi wa jam’iyyar PDP takara a babban zaben 2019 da ya gabata, inda shugaba Buhari ya lashe, ya zauna inuwa daya a daurin auren da tsohon mukarrabin sa uban jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban narkakkiyar jam’iyyar  ACN Bisi Akande.

Sauran wadanda su ka halarci daurin auren sun hada da gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kazalika an ga gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya da kuma shugaban kwamitin riko na APC gwamna Mai Mala Buni.

Irin wannan taro na aure ko jana’iza a gidajen manyan ‘yan bokon Najeriya kan sa wadanda a fili a ke ganin su na hamaiya da juna zama a inuwa daya, duk da dama a daki su kan zauna tare su yi mu’amalar su amma in sun hau kan dandamalin kamfen ne su kan furta maganganu da talakawa ke son ji na caccakar juna.
Kazalika matan manyan ‘yan bokon kan yi hulda da juna ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya, kabila ko addini ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
30 thoughts on “SIYASA: AUREN ‘YAR NUHU RIBADU YA HADA MANYAN MASU ADAWA DA JUNA WAJE DAYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.