• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ATTAJIRI MUHAMMADU INDIMI YA DANGANTA TABARBAREWAR TSARO DA SHAN KWAYA

Attajirin nan na Najeriya mazaunin Maiduguri Alhaji Muhammadu Indimi ya ce shan kwaya na daga manyan dalilan tabarbarewar tsaro da ya hada da ta’addanci.

A zantawar sa ta musamman da Muryar Amurka, attajirin ya ce matukar mutane ba da farka sun shiga yaki da shan miyagun kwayoyi ba, Allah kadai ya sam ranar tsayawar fitina.

Alhaji Muhammadu ya ce aikin yaki da shan kwayan ya wuce jami’an yaki da sha da fataucin miyagun keayoyi kadai su maganceta, sai duk jama’a sun sanya hannu a yakin don matsalar ta shiga har gidaje tsakanin mata.

Indimi ya ce lamarin da kan sanya matasa du dau makamai su iya barazana ga rayukan sauran ‘yan kasa na da nasaba da yanda su ka fita daga hayyacin su ne a sakamakon shan kwaya.

A bangaren jami’an hukumar yaki da shan miyagun kwayoyin ta Najeriya NDLEA na cewa kullum masu fataucin kwayar kan sauya dabara don isar da miyagun kwayoyi ga masu sha a duk yanda a ka samu rintsi ko daukar matakai madu tsauri.

Hamisu Lawan shu ne babban jami’in hukumar a Abuja.

Sabon shugaban hukumar NDLEA Janar Buba Marwa ya lashi takobin sa kafar wando daya da fataken kwaya daidai lokacin da masu sha ke kara gano wasu sabbin dabaru  samun abubuwan da za su rika sanya su jin tamkar su na duniya hodar iblis ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
10 thoughts on “ATTAJIRI MUHAMMADU INDIMI YA DANGANTA TABARBAREWAR TSARO DA SHAN KWAYA”
  1. I think thiss is one of the most important information for me.
    And i am glad reading your article. Butt wanna remark on few general things, The web site style is perfect, the articles is really
    great!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *