Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar zai aiyana tsayawa takarar shugaban Najeriya a zaben 2023,
Atiku wanda zai gabatar da taron aiyanawar a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja wato CONFERENCE CENTER, ya gudanar da taro da manema labaru kan takarar da zai yi a inuwar babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Atiku wanda ya yi wa PDP takara a 2019 amma shugaba Buhari ya yi nasara a kan sa, ya ce ya ke dawowa batun takarar don yanda tsaro da talauci ya addabi ‘yan Najeriya.
Tsohon dan takarar ya danganta rashin tsaron da rashin nagartaccen shugabanci.
PDP da sauran jam’iyyu za su gudanar da zaben fidda gwani a watan mayu.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Free submission of your new website to over 1000 business directories here https://bit.ly/submityoursite1000