• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ATIKU ABUBAKAR YA LASHE ZABEN FIDDA GWANI NA PDP

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe tikitin zaben shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP.

Shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya mika tutar PDP ga Atiku Abubakar bayan aiyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Tun tinkaro filin wasan na kasa da ke Abuja na Moshood Abiola za ka ji a na ambatar sunan Atiku kafin jin sunan wasu daga ‘yan takarar.

An kada kuri’u 767 inda Atiku ya samu 371 mai bi ma sa baya gwamnan Ribas Nyesom Wike ya samu kuri’u 237 sai tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da ya zo na uku da kuri’u 70.

Magoya bayan Atiku sun kaure da farin ciki da nuna lokaci ya yi da za su ke da kwarin guiwar amsar madafun iko.

Nasarar Atiku ta yi armashi da janyewar gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal wanda ya marawa Atikun baya.

Dan kwamitin labarun zaben Yusuf Gingyadi ya ce Tambuwal ya yi hakan ne don kishin cigaban PDP.

Yanzu za a zuba ido kan jam’iyyar APC da za ta gudanar zaben fidda gwani a litinin mai zuwa bayan dage ranaku da ta rika yi da masu sharhi ke cewa don sanin wa PDP za ta tsayar ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.