• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ASUU-KOTUN MA’AIKATA TA DAGE SAURARON KARAR DA GWAMNATI TA SHIGAR

ByYusuf Yau

Sep 13, 2022

Kotun ma’aikata ta dage sauraron karar da gwamnatin taraiya ta shigar da kungiyar malaman jami’a ASUU don tilasta ma ta janye dogon yajin aikin da ta ke ciki a halin yanzu.

Bayan sauraron bangarorin biyu daga lauyoyin su Tijjani Gadzali da ke wakiltar gwamnati da Femi Falana mai wakiltar ASUU, alkalin kotun P.I. Hamman ya dage cigaba da sauraron karar zuwa 16 ga watan nan.

Alkalin ya bukaci bangarorin biyu su rubuto bayanan su don gabatarwa ga kotu, kuma ya ce shi ya na aiki ne a matsayin alkalin lokacin hutu, don in an dawo hutu za a tura karar ga alkalin da zai cigaba da aiki a kan ta gadan-gadan.

Malaman jami’ar na nuna bacin rai kan matsayar gwamnati ta su dawo aiki ba tare da biyan su albashin watannin da ba su yi aiki ba.

Kazalika malaman na cigaba da nuna laifin na gwamnati ne don rashin cika alkawarin yarjejeniyar da a ka yi ta cimmawa ta sulhu a baya tun daga shekara ta 2009.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “ASUU-KOTUN MA’AIKATA TA DAGE SAURARON KARAR DA GWAMNATI TA SHIGAR”
  1. Pelvik boşluğun destek yapıları tehlikeye girdiğinde
    bir sistosel veya prolapseli mesane oluşur.
    Pelvik boşluğun içeriği normal anatomik pozisyonunu koruyamaz ve vajina gibi çevredeki içi boş
    organlara herniasyon yapamaz. Bu genellikle düşmüş bir
    mesane olarak bilinir ve bunun gerçekleştiği süreç kadınlarda düşmüş mesane altında daha fazla açıklanır.

Leave a Reply

Your email address will not be published.