• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ASUU-AKWAI BARAZANAR SHIGA YAJIN AIKIN ‘YAR GABA DAYA

Da alamu kungiyar malaman jami’ar Najeriya ASUU na shirin aukawa yakin aikin har illa masha Allahu don korafin rashin cika alkawarin gwamnatin Najeriya.

Kungiyar dai da ta fara yajin aikin gargadi na kimanin mako daya har ya kai ta ga aukawa na tsawon wa’adi don cigaba da magana da gwamnati kan yarjejeniyar da a ka cimma tun 2020.

‘Yan kungiyar sun fara harbin iska na nuna shirin daura damarar gagarumin yajin aiki kamar wanda su ka yi a bariya na tsawon wata 9.

Daya daga ‘yan kungiyar Dr. Kabiru Danladi Lawanti ya rubuta a shafin sa na yanar gizo cewa shirin aukawa yajin aikin ya kai kashi 98%.

Zai yi wuya dama a shekara lafiya ba barazanar yajin aikin malaman jami’a a Najeriya da hakan kan gurgunta lamuran ilimi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.