• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ASO ROCK NA NUNA RASHIN KISHIN KASA KE SA WASU SUKAR NAJERIYA A KETARE

Fadar gwamnatin Najeriya Aso Rock ta ce son zuciya da rashin kishin kasa ke sa wasu zabar maganganu a ketare da ke taba kimar Najeriya da barazana ga dimokradiyya.

Aso Rock ta ce masu maganganun kan karawa bayanan da su ke yi gishiri ko yin amfani da damar don jan hankalin manyan kasashen duniya su rika daukar Najeriya a matsayin kasa da ba a mutunta bambanci addini da kabilanci.

Aso Rock na magana ne kan dabi’ar wasu ‘yan Najeriya irin Reno Omokri da kan shirya zanga-zanga a ketare don cin zarafin shugaba Buhari da kuma kwanan nan jawabin shugaban darikar katolika na Sokoto Bishop Matthew Hassan Kukah da ke nuna gwamnatin ba ta tabuka komai kan tsaro yayin da ‘yan ta’adda musulmi ke kashe mabiya addinin kirista. 

Gwamnatin dai da tun farko ta zaiyana kalaman Bishop Kukah ta yanar gizo ga majalisar dokokin Amurka da cewa soki burutsu ne, ta ce kowane dan kasa na da hakkin kare kasar sa don ba wata kasa da za ta gyarawa wata kasa illoli sai dai in akwai wani muradi da a ke son cimmawa.

Kukah dai a jawabin na sa ya ce kiristoci ke da ilmi da kuma wasu musulmi na wasu kabilu don haka akwai bukatar Amurka ta taimkawa ta kokarin majami’a na bunkasa ilimi don akwai zawarawa da almajirai na gararamba kusan su miliyan 15-16 wadanda jahilci ke damun su inda kashi 80% 90% musulmi ne.

A can baya dai kafin wannan sabuwar matsaya Bishop Kukah ba ya alakanta ta’addanci ga wani addini. Ga ma matsayar ta sa a baya.

Kukah ya ce a karo na farko an samu duk masu rike da ma’aikatar tsaro musulmi, hakanan majalisar dokokin taraiya da ke da shugaban dattawa musulmi na wakilai ma kazalika; duk da haka Kukah ya ce ba wai musulmi na samun wata garaba ba ce su ma tamkar wahalallu ne masu yake da shigen dariya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
1,973 thoughts on “ASO ROCK NA NUNA RASHIN KISHIN KASA KE SA WASU SUKAR NAJERIYA A KETARE”