• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ASARAR ‘YAN KASUWAR AREWA-MUN HADA RAHOTO MU NA BUKATAR DIYYAR NAIRA BILIYAN 47

ByHassan Goma

Oct 22, 2021

Kungiyar ITTIFAKIN AREWA wato “northern consensus” ta kammala hada rahoto a kan irin asarar da ‘yan kasuwar arewa su ka yi a kudancin Najeriya musamman a sanadiyyar zanga-zangar endsars.
Rahoton da a ka tsara shi a wani kundi da ke dauke da hotunan wadanda a ka kashe da dukiyoyin da a ka kona kurmus: na bukatar diyyar Naira biliyan 47 ne.
Shugaban kungiyar ITTIFAKIN AREWA Dr.Auwal Aliyu Abdullahi ya ce za su mika rahoton ga fadar Aso Rock wacce tun farko ta yi alkawarin daukar matakin ba da diyyar kashi 10%.
Dr.Abdullahi ya kara da cewa a lokacin da a ka samu kona kasuwar Sasa a Ibadan jihar Oyo har ya kai ga ‘yan kasuwar arewa sun dakatar da kai hajar su kudu, gwamnati ta wakilta gwamnan Kogi Yahaya Bello wanda ya zauna da su da daukar alwashin ba da diyya.
Cikin shawarwarin hana aukuwar akasin a gaba har da kafa kasuwannin shiyya a kan iyakar arewa da kudu don duk mai bukatar muhimman kaya ya zo wajen ya yi cinikin sa.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na arewa reshen Abuja Adamu Hassan ne ya jagoranci tattara rahoton da nuna kwarin guiwar gwamnati za ta cika alkawari.
Illar da a ke samu ita ce rashin hadin kan fataken kaya daga arewa zuwa kudu da wasun su kan zulle su tafi da haja kudu don cin kazamar riba yayin da a ka dau matakin yajin kai kayan don tilasta inganta lamuran tsaro.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.