• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ASABAR DIN NAN TA KE RANAR IDIN BABBAR SALLAH A DUNIYA

ByNoblen

Jul 8, 2022

Asabar din nan musulmi a duniya ke murnar idin babbar sallah inda masu halin yin yanka kan yanka dabbobi kama daga raguna, shanu har zuwa soke rakuma.

Yankan dai ya samo asali ne daga zamanin Annabi Ibrahim yayin da ya yi mafarkin ya na yanka dan sa inda ya yi azamar yanka dan sa na sa Annabi Isama’il amma Allah ya fanshe da rago.

Hakika dabobin yanka sun yi matukar tsada a nan Najeriya inda a ka ba da labarin sayar da wani rago Naira dubu 400 a Abuja.

Farashin raguna a Abuja ya kama daga Naira dubu 150 zuwa 250 har mafi girman raguna ta hanyar yanda a ka gudanar da ciniki.

A gaskiya a wasu sassan kuma sai mutum ya ware Naira dubu 100 kafin samun rago mai ma’ana.

A na fatan gudanar da idin lami lafiya da yin ziyarce-ziyarce da ba da kyautuka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.