• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ARZIKIN NAJERIYA-RIJIYA TA KAWO RUWA GUGA TA HANA-ALHAJI SHEHU ASHAKA

 

Dan kasuwa kuma daya daga dattawan arewa Alhaji Shehu Ashaka ya ce Najeriya ta na arziki amma ya na makalewa ne hannun wasu kalilan.

A zantawa ta musamman da a ka yi da shi kan cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yanci, Alhaji Ashaka ya ce arzikin tamkar rijiya ta kawo ruwa guga ta hana don yanda wasu su ka mallake dukiyar daga su sai ‘ya’yan su.

Don haka dattijon ya yi gargadin cewa matukar masu babakere ba su sauya hali ba, to za a wayi gari su yi nadamar rashin kyautatawa da su ka yi.

Cikin matukar takaici Alhaji Ashaka ya ce yau an wayi gari a arewa a na sayar da buhun masara Naira dubu 26 kuma wai a ce talakawa ba za su koka ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *