• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AREWA NA DAUKAR MATAKAN KARFAFA BURT’ALI DA DAZUKAN KIWO

Da alamu akasarin gwamnonin arewacin Najeriya na daukar matakan maslaha kan lamuran makiyaya ta hanyar ware dazukan kiwo.
Tuni wasu jihohin su ka ware dazuka don makiyayan biyo bayan shirin gwamnatin taraiya na farfado da burtali.
Dama a na daukar makiyayan da ke tafiya kudancin Najeriya da cewa ‘yan arewa ne duk da wasun su a kudu a ka haifi kakannin su.
Duk da haka a na samun turjiya daga kalilan daga jihohin na arewa inda Binuwai ce karkashin gwamna Samuel Otom ta hana ba da fage don kiwo a fili.
Wani kalubalen da gwamnonin za su warware shi ne yanda wasu mutane su ka cinye tsoffin burtalin shanu su ka maida su filaye da gonaki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *