Jam’iyyar APGA ta Ojukwu ta cigaba da samun tagomashi a zaben jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Sakamakon kurii’un bai zama abun mamaki ba in an duba yanda ‘yan Biyafara ke gudanar da kamfen din aware a yankin.
Dan takarar jam’iyyar APGA kuma tsohon gwamnan babban banki Charles Soludo ya lashe kusan dukkan kananan hukumomin jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Nkem Okeke wanda ya sauya sheka daga APGA zuwa APC bai samu lashe zaben ba a mazabar sa ga dan takarar APC Andy Uba.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀