Jam’iyyar APC ta sanya ranar 23 ga watan nan ta zama ranar tantance ‘yan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar.
Zuwa yanzu ‘yan takara 28 ne su ka cike fom din takara don zaben fidda gwani da jam’iyyar za ta gudanar daga ranar 28 ga watan nan.
Kalilan daga masu son takarar sun janye musamman don rashin son rasa mukaman su a gwamnatin shugaba Buhari.
Da alamun jam’iyyar ta tara biliyoyin Naira ta hanyar sayar da takardun takarar masu dan karen tsada.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀