• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

APC-WASU GWAMNONI SUN YI TUTSU DA NUNA LALLAE SHUGABA BUHARI YA BUKACI A SAUKE MALA BUNI

Wasu gwamnoni sun yi tutsu a jam’iyyar APC mai mulki a taraiya inda su ke bukatar kawar da shugaban kwamitin rikwan jam’iyyar Mai Mala Buni.
Akalla daya daga gwamnonin ya ce umurni ne daga shugaba Buhari na kawar da Mai Mala, wanda shi ma gwamna ne da nada gwamnan Neja Abubakar Sani Bello.
A gefe guda wasu gwamnonin na APC sun yi mubaya’a 100% ga Mala Buni da nuna matukar a ka taba shi gabanin babban taron jam’iyya, za a iya samun matsala.
A zahiri ko a badini an samu rabuwar kawuna tsakanin gwamnonin jam’iyyar da hakan barazana ce ga karfin jam’iyyar a babban zaben 2023.
A irin wannan yanayi, za a yi tsammanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar za su zauna su sulhunta kan su da rage burin kashin kan matukar jam’iyyar za ta cigaba da tasiri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “APC-WASU GWAMNONI SUN YI TUTSU DA NUNA LALLAE SHUGABA BUHARI YA BUKACI A SAUKE MALA BUNI”
  1. Hi there! I just want to give you a big thumbs up for the great info you have got right here on this post.
    I will be returning to your web site for more soon.

Leave a Reply

Your email address will not be published.