• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

APC TA TSAWAITA RANAKUN SAYEN FOM DIN TAKARA DA KWANA BIYU

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tsawaita lokacin sayen fom din takarar mukamai don shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Dan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar Dattuwa Ali Kumo ya ce bukatar a kara wa’adin daga masu son sayan fom din ya jawo daukar matakin.
Yanzu dai za a rufe sayar da fom din zuwa alhamis din nan 12 ga watan nan na mayu.
APC ta ce za ta karbi dukkan takardun da a ka cke ranar jumma’a yayin da za ta fara tantance takardun ranar asabar din nan.
Jam’iyyar dai ta tara biliyoyin Naira daga sayar da fom din musamman na takarar shugaban kasa da darajar sa Naira miliayn 100.
Hakika wannan shi ne karo da ya samu yawan mutane da su ka sayi fom din takarar zaben fidda gwani kuma ya zama fom din ya fi kowane lokaci tsada.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.