• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

APC TA SANYA NAIRA MILIYAN 20 A MATSAYIN KUDIN FOM DIN TAKARAR SHUGABANCIN JAM’IYYA

ByNoblen

Mar 17, 2022

Jam’iyyar APC ta fitar da sanarwar kudin sayan fom Naira miliyan 20 don takarar shugaba yayin da mataimakin shugaban jam’iyyar Naira miliyan 10 ne.
Duk sauran mukamai Naira miliyan 5.
A alamun da ke nuna jam’iyyar da ke karagar mulki a Najeriya ta fara shirya babban taron ta a 26 ga watan nan shi ne fitar da wannsn sanarwa da ta biyo bayan raba mukamai ga shiyyoyi inda yankin arewa ta tsakiya zai samar da sabon shugaban jam’iyyar.
Dukkan manyan ‘yan takarar a shiyyar masu hannu da shuni ne da su ka hada da tsoffin gwamnoni da dan majalisar dattawa Sanata Sani Musa da ke cewa ya shirya a shata dagar zaben.
Musa na martani ne kan raderadin tsayar da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban.
Muhammad Sa’idu Etsu shi ne mafi karancin shekaru a ‘yan takarar; ya ce shi ma a shirye ya ke wajen samo kudin fom din.
A na sa bangaren mai neman takarar shugaban matasa Abdullahi Sidi Ali da tsarin shiyya ya sa ya koma neman mataimakin shugaban matasan, ya koka cewa an zumbula kudi.
Ya zama abu mai muhimmanci jam’iyyar ta kawar da umurnin kotu na dakatar da babban taron da kuma rage tsamar gwamnoni matukar taron zai yiwu kuma ba zai bar baya da kura ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “APC TA SANYA NAIRA MILIYAN 20 A MATSAYIN KUDIN FOM DIN TAKARAR SHUGABANCIN JAM’IYYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.