• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

APC TA DAWO DA ZABEN FIDDA GWANI BAYA DA KWANA DAYA A KARSHEN WATAN NAN

Jam’iyyar APC da ke da da gwamnatin taraiya a yanzu ta dawo da babban taron fidda gwani don tsaida dan takarar shugaban kasa baya da kwana daya a karshen watan nan.

Taron da zai dauki kwana uku, zai fara ne daga ranar 28 zuwa 30 ga watan nan maimakon yanda ya ke a baya daga 29 zuwa 1 ga watan gobe.

Dan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar Dattuwa Ali Kumo ya ce sun matso da lokacin baya ne don sun samu tabbacin jam’iyyar PDP ba za ta gudanar da taron ta a dandalin EAGLE SQUARE da ke Abuja ba, za ta gudanar da na ta a Lagos.

Game da tsarin zaben, Kumo ya ce sai an je wajen zaben ne za a tantance hanyar da za a gudanar da zaben wa imma ta kada kuri’a ko daidaitawa.

A jumma’ar nan APC ta rufe karbar takardun fom da a ka cike don shiga takarar inda a asabar din nan za a tantance takardun.

In a na bin labaru shugaba Buhari ya umurci duk masu rike da mukaman majalisar sa ta zartarwa da ma gwamnatin babban bankin Najeriya da ke sha’awar takarar mukamai, su yi murabus kafin ranar litinin 16 ga watan nan na Mayu.

Hukumar zabe za ta karbi jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyu na zaben 2023 zuwa ranar 3 ga watan gobe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.