• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

APC TA DAGE TANTANCE ‘YAN TAKARAR TA NA SHUGABAN KASA

Jam’iyyar APC mai mulki a taraiyar Najeriya ta sanar da dage zaman tantance ‘yan takarar shugaba kasa kusan su 25 a inuwar jam’iyyar.

Tun farko jam’iyyar ta aiyana za ta gudanar da tantancewar a litinin din nan 23 ga watan nan na Mayu.

Sakataren labarum jam’iyyar Felix Morka ya fitar da sanarwar da baiyana cewa za a sanar da sabuwar ranar tantancewar nan gaba kadan.

Ko ma dai me ya jawo dage tantancewar, jam’iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan takarar zuwa karshen watan nan.

Hukumar zaben Najeriya INEC za ta karbi jerin sunyaen ‘yan takarar dukkan jam’iyyu zuwa ranar 3 ga watan gobe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “APC TA DAGE TANTANCE ‘YAN TAKARAR TA NA SHUGABAN KASA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.