• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

APC TA DAGE BABBAN TARON TA DA WATA DAYA

Jam’iyyar gwamnati APC ta sanar da dage babban taron ta na zaben sabbin shugabanni da tsawon wata daya daga ranar da a ka tsara gudanar da taron a 26 ga watan nan.
Yanzu jam’iyyar ta ce za ta gudanar da taron a ranar 26 ga watan gobe.
Bayan taron masu ruwa da tsaki APC karkashin Mai Mala Buni ta ce za ta yi amfani da ranar 26 ga watan nan wajen gudanar da zaben shiyyoyi, duk da ba ta fadi dalilan manta gudanar da wadannan taruka ba.
Dambatta ya ce za a yi amfani da ranaku gabanin ranar babban taron wajen tantance ‘yan takarar daga shiyyoyi har ma da karbar korafi don gudanar da taron ba da barin baya da kura ba.
Daraktan ya kara da cewa ba wata tababa game da sabuwar ranar “in Allah ya yarda ina ji a rai na ba za a samu matsala ba a sabuwar ranar kuma za a gudanar da taron a dandalin taruka na EAGLLE da ke Abuja.”
Tuni a ka fara samun martani tsakanin masu ganin a jira don akwai takamemmen lokaci da masu cewa ba su da kwarin guiwar ba za a sake dagewa daga sabuwar ranar ba.
Jam’iyyar APC da ta faro mulki daga shekara ta 2015 na fafutukar neman zarcewa da mulki idan shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya kammala wa’adi a 2023.
Baya ga babbar jam’iyyar adawa PDP da a baya ta yi mulki na tsawon shekaru 16, akwai bayanan da ke nuna manyan ‘yan siyasa da ba su gamsu da tafiyar manyan jam’iyyun biyu ba, na shirin kafa sabuwar jam’iyya don neman amsar ragamar mulki a zaben mai zuwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “APC TA DAGE BABBAN TARON TA DA WATA DAYA”
  1. Hi my friend! I want to say that this post is awesome, nice written and
    include approximately all significant infos. I would like to look
    extra posts like this .

  2. Somebody necessarily assist to make significantly articles I would state. This is the very first time I frequented your web page and up to now? I amazed with the research you made to make this actual publish extraordinary. Excellent task!

Leave a Reply

Your email address will not be published.