• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ANYI WA ‘YAN HOUTHI DIRAR MIKIYA

An caccaki ‘yan tawayen houthi a Yaman da Iran ke marawa baya don mutuwar ma’aikacin ofishin jakadancin Amurka a hannun su.

Ofishin jakadancin ya fitar da sanarwar mutuwar ma’aikacin mai suna Abdulhamid Al-Ajami a hannun ‘yan tawayen.

‘Yan houthi sun sace Al-Ajami a bara inda ya riga mu gidan gaskiya yayin da ya ke kulle a wajen su.

Ofishin jakadancin ya yi tir da yanda houth ta rike Al-Ajami har ya mutu nesa da iyalin sa a matsayin na dattijon da ke da jikoki.

Don haka ofishin ya bukaci ‘yan tawayen su sako sauran ma’aikatan ofishin da su ka garkame don komawa wajen iyalin su lafiya.

An samu labarin ‘yan houthi sun ganawa Al-Ajami azaba da hana shi samun kulawar likita har hakan ya yi sanadiyyar rasa ran sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.