• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ANNOBAR KORONA TA SA AN AIBATA NI A CAN BAYA-SADIYA UMAR FARUQ

Ministar jinkai ta Najeriya Sadiya Umar Faruq ta baiyana cewa rikicewar mutane lokacin annobar korona ta sa su ka kasa ganin alherin da ta kawo daga ofishin ta.
In za a tuna an zargi Sadiya da rashin tabbatar da tallafi ya isa ga jama’a, rashin sahihancin bayanai ciyar da dalibai a makarantu don lokacin ma ba a zuwa makaranta da kuma rashin isar kudin tallafi Naira dubu 20 don ragewa jama’a radadi.
A taron karbar kyautar girmamawa daga wani asusu mai suna DUSUSU, Sadiya ta ce tsanantar rikicewar mutane ta sa ba a ganin alherin da ta shuka, inda ga shi yanzu wani asusu ya zo daga ketare ya karrama ma ta da lambar yabo.
Ministar ta kara da cewa ko a lokacin da a ke sukar ta, ba ta aikata wani abun da ba daidai har kuma zuwa yanzu da ta ke ganin Allah ya wanke ta daga zargi.
Sadiya Farouk ta ce za ta cigaba da aiyukan tallafawa marar sa karfi a al’umma har zuwa karshen mukamin da a ka ba ta.
Daya daga mukarraban ta, marubuciya Hannatu Musawa ta ce ba wata minista a gwamnatin Buhari da ta aikata abun kirki tamkar Sadiya Faruq.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
57 thoughts on “ANNOBAR KORONA TA SA AN AIBATA NI A CAN BAYA-SADIYA UMAR FARUQ”

Leave a Reply

Your email address will not be published.