• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ANNOBA-GWAMNATIN NAJERIYA TA DAKATAR DA AIKIN MA’AIKATA DAGA MATAKIN ALBASHI NA 12 ZUWA KASA

BySafina Sadisu Mahmoud

Dec 22, 2020

A dalilan rahotannin da gwamnatin ta bayar cewa cutar annobar korona na karuwa, yanzu gwamnatin ta ba da umurnin dakatar da aikin ma’aikata daga matakin albashi na 12 zuwa kasa har nan da makwanni 5.

Sakataren gwamnatin Boss Mustapha ya baiyana haka a matsayin sa na shugaban kwamitin shugaba Buhari na yaki da cutar ta annoba.

Mustapha ya ce shugabannin ma’aikatu da manyan sakatarori ne za a kama da laifi in an samu saba ka’idojin kariya daga cutar ta korona.

Mustapha ya ce hatta ‘ya’yan sa sun kamu da cutar inda shi ya tsallake rijiya da baya don ya na garkama takunkumi a fuskar sa koda a gida ne.

Da alamu wannan na nuna gwamnatin ka iya daukar matakin takaita zirga-zirga a tsakanin sauran jama’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ANNOBA-GWAMNATIN NAJERIYA TA DAKATAR DA AIKIN MA’AIKATA DAGA MATAKIN ALBASHI NA 12 ZUWA KASA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.