• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ANA ZAMAN ZULLUMI BIYO BAYAN HUSATAR PALASDINAWA DON TAKURA SU A BIRNIN KUDUS

ByNasiru Adamu El-hikaya

Apr 25, 2021

Yanzu haka a na zaman zullumi don yanda Palasdinawa su ka fusata bisa takura su da aka yi a birnin kudus da ya hada da masallacin Aqsa mai daraja tsakanin musulmi, kirista da yahudawa.

Tuni a birnin Gaza ‘yan Hamaz su ka harba wasu rokoki cikin yankin Israila da gargadin kar Israila ta sanya hakurin su ya kare.

Tuni kamar yanda a ka saba, Israila ta yi amfani da tankunan yaki da hare-haren samaniya kan yankunan Hamaz a Gaza.

Zuwa yanzu ba labarin rasa rayuka a bangarorin biyu.

Ofishin jakadancin Amurka da tsohon shugaba Donald Trump ya kauro da shi birnin kudus daga Tel’aviv ya bukaci a maida zuciya nesa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
59 thoughts on “ANA ZAMAN ZULLUMI BIYO BAYAN HUSATAR PALASDINAWA DON TAKURA SU A BIRNIN KUDUS”

Leave a Reply

Your email address will not be published.