• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ANA YI WA SHUGABA BUHARI FATAN SAMUN SAUKI

ByYusuf Yau

Mar 31, 2021

Jama’a na baiyana fatar samun waraka ga shugaba Buhari a yayin da ya nufi London don ganin likita.
Mutane da dama sun shiga shafukan su na yanar gizo su na fatar samun lafiya ga shugaban mai shekaru 78 a duniya.

Shugaban dai ya kwan biyu bai je duba likita ba kan jinyar da ta ke damun sa.
Jinyar da ta fi fice ga shugaban ita ce ciwon kunne da kan sa sai ya saurara sosai ya fahimci abun da a ke fada ma sa.

Sanarwar ta nuna shugaban zai yi kimanin mako biyu ne a London kafin dawowa Abuja.
Hakanan sanarwar ta ce duba lafiyar sa za a yi, ba ta faiyace ko kan wani ciwo ba ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *