Akalla ‘yan Taliban sun hallaka dan zanga-zanga daya a zanga-zangar da wasu mutane su ka shirya a birnin Jalalabad na Afghanistan.
Masu zanga-zangar dai na son lalle sai a cire tutar ‘yan Taliban daga gine-ginen gwamnati a sa ta Afghanistan.
Hakanan wasu masu zanga-zanga dauke da tutar kasar sun samu raunuka a sanadiyyar harbi don tarwatsa tunzurin na mutane ga sabuwar gwamnatin kasar.
Wani faifan bidiyo ya nuna hoton masu zanga-zanga dauke da tutar kasar na tafiya kan titi su na wakar kishin kasa, sai kwatsam a ka ji karar harba bindiga da ya jama’a su ka arce daga bigiren don tsira da ran su.
A Kabul Amurka na cigaba da jigilar jama’ar ta da kuma ‘yan Afghanistan da ke mubaya’a ga lamuran ta.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACIššš
Hey there this is somewhat of off topic but I was wanting to
know if blogs use WYSIWYG editors or if you have to manually code with
HTML. I’m starting a blog soon but have no coding know-how so I wanted
to get guidance from someone with experience. Any help would be greatly appreciated!