A na cigaba da ta’aziyyar rasuwar tsohon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Alhaji Gambo Jimeta.
Marigayin ya rasu bayan fama da jinya a Abuja inda a ka gudanar da jana’izar sa da makwanci a makabartar Gudu Abuja.
Alhaji Jimeta ya na daga tsoffin shugabannin ‘yan sanda da su ka shahara a fagen aikin da su ka hada su marigayi Ibrahim Coomassie, Muslihu Smith da sauran su.
Daya daga alarammomi na JIBWIS Saifullah Umar Kira ya ce marigayin na sha’awar sauraron karatul Alkur’ani mai girma.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀