Binciken da a ka gudanar a hukumar kula da yankin Neja Delta ya gano cewa akwai aiyuka dubu 13 da a ka yi watsi da su a yankin tun kafa hukumar.
Ministan Neja Delta Godswill Akpabio ya baiyana haka ga shugaba Buhari a rahoto ta hanyar ministan shari’a Abubakar Malami.
Yayin da a ke aikin rahoton, wasu ‘yan kwangila sun dawo su ka kammala aikin tituna 77.
Ministan ya ce binciken ba ya nufin tona asirin wani mutum, sai dai gano yanda a ka kashe makudan kudin da a ka zuba a hukumar.
Hukumar ta karbi Naira tiriliyan 6 a tsawon shekarun 19 da a ka kafata amma ba tasirin aikin a yankin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀