• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI WA MATUKIN JIRGIN SAMA KISAN GILLA A KADUNA

An samu gawar dan Sanata Bala Ibnu Na Allah wato Kaftin Abdulkarim a mace a gidan sa da ke Malali Kaduna.

Marigayin dai shi ne babban dan Sanata Na Allah.

Marigayin mai shekaru 36 ya gamu da ajalin sa inda masu aikata kisan gillar su ka daure shi kafin yin kisan, inda daga nan su ka dauke dukiyar sa mai daraja ciki har da mota su ka tafi.

Labarin dai ya nuna miyagun sun shiga gidan Abdulkarim ta baya inda su ka yi amfani da rufin gidan wajen isa sashen da marigayin ya ke.

Jami’an tsaron makwabta ne su ka lura da marfin kofar gidan a bude, inda daga nan a ka samu gawar marigayin.

Sanata Na Allah na da ‘ya’a uku kuma duk direbobin jirgin sama ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.