• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI TARON TUNAWA DA MAZAN JIYA A NAJERIYA

Kamar yanda a ka saba duk shekara an gudanar da taron tunawa da mazan jiya a Najeriya da yin faretin karramawa.
Taron a dandalin dogon yaro da ke daura da dandalin taro na EAGLE, na alamta tunawa da sojojin da su ka rasa ran su a fagen daga musamman zamanin yakin basasar Najeriya.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya aza furanni da bude wani keji inda fararen tattabaru su ka tashi sama da ya ke nuna zaman lafiya.
A bara, tsoffin sojoji sun gudanar da zanga-zanga a Abuja don kokawa ga rashin samun hakkokin su na fansho da ladar ajiye aiki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.