• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI KARIN GISHIRI KAN TARON DA A KA CE AN YI A 2010 KAN YAKOWA-REVEREND HAYAB

Shugaban kiristoci na Najeriya CAN reshen jihar Kaduna Reverend John Hayab ya nuna an yi karin gishiri kan wani taro da a ke ce an yi a Bauchi a 2010 karkashin jama’atu nasril islam da wai a ka shirya hallaka tsohon gwamnan Kaduna Ibrahim Yakowa.

Hayab ya ce takardar bayan taron da ta ke yawo tun 2010 kuma ta ke nuna ministan sadarwa Dr.Isa Pantami ya jagoranci taron, an yi karin gishiri.

Shugaban na mabiya addinin kirista a Kaduna na magana ne da gidan jaridar yanar gizo na Premium Times.

Hayab wanda ya rike mukamin mai taimakawa gwamna Yakowa kan lamuran addini, ya ce ya na kusa da marigayin kuma ba haka lamarin da a ka yada a takardar ya ke ba.

Malamin na kirista ya bukaci jami’an tsaro su yi hanzarin daukar mataki kan wannan batu don hana tada fitina.

Hayab ya ce a yi sauri a yaiyafawa wannan fitina ruwa.

In za a tuna Gwamna Yakowa ya riga mu gidan gaskiya a hatsarin jirgi mai saukar angulu a jihar Bayelsa tare da tsohon mai ba da shawara kan tsaro Andrew Azazi a 2012.

Yakowa na dawowa ne daga jana’izar mutuwar mahaifin mai taimakawa tsohon shugaba Jonathan , Oranto Doughlas.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “AN YI KARIN GISHIRI KAN TARON DA A KA CE AN YI A 2010 KAN YAKOWA-REVEREND HAYAB”
  1. At this time it looks like WordPress is the top blogging platform available right now.
    (from what I’ve read) Is that what you are using
    on your blog?

  2. Everything is very open with a clear explanation of the issues.
    It was definitely informative. Your site is very useful.
    Thank you for sharing!

Leave a Reply

Your email address will not be published.