Jama’a sun taru a Kaduna don jana’izar marigayi tsohon gwamnan jihar Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa wanda ya rasu bayan fama da jinya ya na mai shekaru 84.
Marigayin wanda ya yi gwagwarmaya don dawowar mulkin farar hula bayan dogon mulkin soja, ya kasance a bangaren hamaiya a siyasar sa da son tsari na talakawa ko salon mulkin gurguzu na kasar Rasha daga jagororin salon su Karl Marx, Vladimir Lenin, Frederick Engles, Fidel Castro, Mao Tsetung da sauran su.
Marigayin ya taba yin wata mujalla mai suna fitina da ta rika yayata labarun talakawa da da yakar salon mulkin jari hujja.
A wani yanayi mai sarkakiya, an tsige Balarabe Musa daga kujerar gwamnan Kaduna inda Abba Musa Rimi ya haye kujerar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna juyayin rasuwar Balarabe Musa.