• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI JANA’IZAR GARKUWAN GOMBE SANATA SA’IDU UMAR KUMO A ABUJA

An yi jana’izar Sanata Sa’idu Umar Kumo a Abuja wanda Allah ya yi rasuwa bayan fama da gajeruwar jinya.

Jana’izar marigayin ta gudana ne a babban masallacin Abuja inda kuma a ka yi ma sa makwanci a makabartar Gudu da ke Abuja.

Sanata Kumo wanda shaharerren Dan siyasane ya rike mukamai manya musamman a narkakkiyar jam’iyyar ANPP inda ya zama babban sakatare da yi yi tasiri wajen samun nasarar lashe zaben tsoffin gwamnoni da dama.

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya kan rasuwar marigayin da zaiyana shi da cewa nasarar sake zaben sa ba za ta kammala ba ba tare da ambata sunan Sanata Kumo ba.

Sanata Kumo wa ne ga tsohon ministan Abuja Dr Aliyu Modibbo da tsohon shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin Gombe Lamido Umar Chikaire.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN YI JANA’IZAR GARKUWAN GOMBE SANATA SA’IDU UMAR KUMO A ABUJA”
  1. It’s perfect time to make some plans for the future and it is time to be happy. I have read this post and if I could I want to suggest you few interesting things or advice. Maybe you can write next articles referring to this article. I wish to read more things about it!

Leave a Reply

Your email address will not be published.