• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI JANA’IZAR DAN JARIDA IBRAHIM ABDUL’AZIZ A YOLA

Mutane sun yi dafifi a Yola jihar Adamawa don jana’izar marigayi dan jarida Ibrahim Abdul’aziz wanda ya rasu sanadiyyar hatsarin mota a hanyar Gombe zuwa Bauchi.

Marigayin wanda wakilin muryar Amurka a jihar Adamawa da Taraba kwne, ya samu yabon mutane da dama da nuna mai kwazo ne da saukin kai.

Shugaban JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya zaiyana marigayin da zana mai jarumtaka wajen aiki musamman a lokacinn da harkokin ta’addanci su ka ta’azzara a yankin arewa maso gabar.

Imam Bala Lau wanda ya tuno doguwar huldar su da marigayin da kan kawo ma sa ziyara musamman in ya shigo gida a Jimeta, ya ce marigayin mutumin kirki ne da yin addu’ar Allah ya jikan sa da rahama.

Gwamnatin Adamawa, rundunar ‘yan sanda a jihar da sauran jama’a sun fitar da sakon ta’aziyya ga rashin marigayin da nuna ya bar gibi mai wuyar cikewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.