• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI JANA’IZAR BARKINDO

ByNoblen

Jul 6, 2022

JAMA’A NA NUNA ALHINI KAN RASUWAR BABBAN SAKATAREN OPEC BARKINDO

Jama’a na nuna alhini kan rasuwar babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur Muhammad Sunusi Barkindo.

Marigayin wanda ya rasu bayan gajeruwar jinya, ya samu karammawa daga shugaba Buhari a daren da a ka wayi gari da labarin rasuwar sa.

Muhammad Sunusi Barkindo da a ka haifa a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na da shekaru 63 a duniya inda ya yi aiki har mataki mafi daukaka a lamuran fetur wato zama babban sakataren OPEC.

Barkindo ne na biyu da ya rike wannan mukami a Najeriya bayan marigayi Rilwanu Lukman.

Marigayin zai yi ritaya a watan agusta inda ya ke kan ranngadin bankwana yayin da Allah ya karbi abun sa.

Mallam Abubakar Ali masanin tattalin arziki ne da lamuran fetur, ya ce rashin ya girgiza dukkan ‘yan kasa don irin daukaka sunan Najeriya da marigayin ya yi.

Kazalika Abubakar Ali ya zaiyana Barkindo a matsayin wnda ya samu karbuwa a sassan duniya.

Kungiyar ta OPEC ta fitar da sanarwar ta’aziyya da yabawa gudunmawar marigayin wajen hidima ga kungiyar wajen shekaru 40.

Barkindo makusancin Lamidon Adamawa ne Barkindo Aliyu Mustapha.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.