• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI GAGARUMAR ZANGA-ZANGAR DOGON DAUKEWAR WUTAR LANTARKI A IRAKI

ByNoblen

Jul 11, 2021 , ,

Daruruwan al’ummar Iraki sun gagarumar zanga-zanga a garuruwan kudancin kasar don nuna bacin rai kan daukewar wutar lantarki.

Wani daga ‘yan zanga-zangar mai suna Diaa Wady ya tsaya a gaban cibiyar wutar da ke daf da birnin Karbala ya na cewa sam ba za su bar wajen ba sai an dawo da wuta ko kuma su rufe cibiyar gaba daya.

‘Yan zanga-zangar maza sun yi kukan kura su ka fasa gilashin bayan motar daya daga jami’an wutar don tsananin fusata sa su ka yi.

Yanzu haka a na yanayin zafi ne a Iraki da kan sa mutane shiga halin ni ‘yasu saboda rashin wutar lantarkin da za ta taimaka a kunna fanka ko na’urar sanyi.

Jami’in labaru na hukumar wutar kasar Ahmad Moussa ya ce akwai wanda ke son haddasa fitina a kasar ta kawo tashin hankali.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *