• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YI ADDU’AR ROKON RUWA A DAMAGARAM TA JAMHURIYAR NIJAR

Hukumomi a yankin Damagaram na jamhuriyar Nijar sun jagoranci gudanar da addu’a don rokon Allah ya horewa yankin ruwan sama don gudanar da lamuran noma.

Matakin ya biyo bayan yanda wasu sassa ke samun ruwan, amma yankin na Damagaram kan samu iska ne mai zafi ba tare da ruwan sama ba.

Sultan na Damagaram Alhaji Abubakar Sanda shi ya jagoranci sallar rokon ruwa don yanda damunar ta yi jinkiri.

Sultan Sanda ya bukaci al’ummar yankin su cigaba da addu’a a duk salloli biyar a masallatai don samun taimakon Allah.

Gwamnan Damagaram Isa Musa ma na kan gaba wajen wannan addu’a, ya na mai cewa sun takarkare ga karatun Alkur’ani da yin addu’ar samun ruwa mai albarka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *